23 Agusta 2026 - 23:37
Source: ABNA24
Mutane Uku Ne Su Kai Shahada Ciki Harda Wani Karamin Yaro A Nablus Da Gaza

Wani yaro ɗan Falasdinu a sansanin Askar da ke gabashin Nablus, yayi shahada sakamakon harbin sojojin gwamnatin yahudawa, kuma a hare-hare daban-daban da aka kai a sansanin Al-Nuseirat da garin Al-Zawayda a tsakiyar zirin Gaza, Falasdinawa biyu sun yishahada kuma wasu bakwai sun jikkata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Wata majiya ta lafiya ta shaida wa gidan talabijin na Al Jazeera cewa, wani yaro ɗan Falasdinu ya yi shahada sakamakon harbin sojojin gwamnatin yahudawa a sansanin Askar da ke gabashin Nablus.

Bisa ga wannan rahoto, sojojin mamaya na Isra'ila sun kuma kutsa cikin gidaje da shagunan kasuwanci, kuma sun fara binciken 'yan ƙasa a garin Al-Awja a cikin Al-Ghawr da ke gabashin Yammacin Kogin Jordan.

Wata majiya a asibitin Shahidai Al-Aqsa a zirin Gaza ta kuma ba da rahoton cewa, sakamakon hare-haren gwamnatin yahudawa a sansanin Al-Nuseirat da garin Al-Zawayda da ke tsakiyar zirin Gaza, Falasdinawa biyu sun yi shahada kuma wasu bakwai suka jikkata. Wasu majiyoyi sun kuma ba da rahoton cewa, a harin gwamnatin yahudawa a garin Al-Zawayda, wani yaro yayi shahada.

A gefe guda, majiyoyin gida na Falasdinu sun ce, matsugunan yahudawa suna ci gaba da kewaye gidaje uku na Falasdinu a yankin "Ras al-Ayn" a Qasra da ke arewacin Yammacin Kogin Jordan, kuma sojojin tsaro na gwamnatin mamaya suna hana shiga da fita 'yan ƙasar Falasdinu zuwa wannan yanki. A inuwar yanke sadarwa da waɗannan gidaje, da kuma hana gwamnatin yahudawa aika ruwa zuwa gare su, waɗannan iyalai uku suna fama da matsanancin karancin ruwa.

Haka kuma, sojojin gwamnatin mamaya sun mayar da ɗaya daga cikin gidajen zuwa sansanin soji, kuma sun jefo da kayayyaki da kayan cikin gida ta tagogi.

……………….

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha